Ministan harkokin wajen Sin zai halarci taron ministocin harkokin waje kan batun nukiliyar Iran
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying, ta ce a ranar Alhamis 2 ga watan ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya tashi zuwa birnin Vienna, domin halartar taron ministocin harkokin waje tsakanin kasar Iran, da sauran kasashe 6 da batun nukiliyar ta ya shafa.
Hakan a cewar ta ya biyo bayan muhimmancin da Sin ke dorawa ne game da batun nukiliyar kasar Iran.
Madam Hua ta ce Sin tana fatan kokari tare da bangarorin da wannan batu ya shafa, don gaggauta daddale yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran cikin adalci, da samun moriyar juna daga dukkanin fannoni. (Bako)