in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a tsawaita lokacin yin shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran da tsawon lokaci ba
2015-06-29 09:57:25 cri

Babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro Federica Mogherini ta bayyana a birnin Vienna a jiya Lahadi cewa, ba za a tsawaita lokacin yin shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran na wannan zagaye da tsawon lokaci ba, amma watakila za a tsawaita lokacin yin shawarwarin da wasu 'yan wanaki,inda ta yi fatan za a cimma yarjejeniya game da batun a dukkan fannoni a cikin kwanaki na karshe.

Kasar Iran da kasashe shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa wato Amurka, Britaniya, Faransa, Rasha, Jamus da kasar Sin sun sha yin shawarwari a birnin Vienna don tattauna yadda za a cimma yarjejeniya game da batun a dukkan fannoni kafin ranar 30 ga wata.

Bayan ganawar da ministocin harkokin wajen kasashen bakwai suka yi, Mogherini ta bayyana wa 'yan jarida cewa, ana fatan kammala shawarwarin ne a karshen watan Yuni ko farkon watan Yuli, amma abin da za a yi yanzu shi ne yadda za a canja niyyar siyasa da fahimtar juna don su zama wata yarjejeniya, kuma an gudanar da shawarwari a wannan zagaye bisa tushen abin da aka cimma daidaito a kai a birnin Lausanne. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China