A jiya Alhamis 4 ga wata, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi a wajen taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin, Rasha da Iran,Ya ce, game da halin da ake ciki, Sin ta bayyana cewa, ya kamata a mutunta sakamakon da aka samu a yayin taron Lausanne, wanda aka samu a karkashin kokarin kasashe 6 da batun nukiliya na Iran ya shafa.
Ya ce, ya kamata a ingiza shawarwarin da ke karkashin sakamakon taron Lausanne, ba wai bangarorin daban daban su gabatar da sabuwar bukata ba, don hana batun ya zama mai sarkakkiya, kazalika ma, ya zama dole a dora muhimmanci sosai game da bukatun bangarorin daban daban da kokarta biya bukatunsu, don cimma matsaya guda. A karshe dai, ministan ya ce, ya kamata a daddale yarjejeniya cikin lokaci, don kafa wani tsarin hana yaduwar makamashin nukiliya a duniya, wannan zai amfana ma aikin samar da zaman lafiya da karko a yankin Gabas ta tsakiya,don haka kasar Sin tana fatan ci gaba da taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.(Bako)