Hakan dai na zuwa ne a gabar da wa'adin karshe na tattaunawar da ake yi ke gaf da kammala. A wannan karo an sanya ranar 30 ga watan nan na Yuni ta zamo ranar kashe ta cimma matsaya. A baya an gaza cimma matsaya game da Nukiliyar kasar ta Iran, a tattaunawar da aka gudanar har karo biyu.
Kudurin da 'yan majalissar dokokin kasar ta Iran suka cimma ya kunshi burin cirewa kasar dukkanin takunkumi, da zarar kasar ta fara cika nata sharudda.
Kaza lika 'yan majalissar sun bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, da ta kaucewa neman bayanai daga sassan soji, da na tsaron kasar, tare da sauran bangarorin sirri da basu shafi Nukiliya ba. Kudurin ya kuma ce Iran za ta amince da matsayar da aka cimma ne kawai, idan har an amince da wadannan sharudda.
Kasashen yamma dai sun dade suna nuna damuwa game da shirin Iran na bunkasa Nukiliya, koda yake Iran din ta kafe cewa shirinta a fannin bunkasa Nukiliya ya shafi harkokin bunkasa rayuwa da ba na soji ba ne.