Ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, da takwaran sa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, sun gudanar da sabbin shawarwari cikin sirri, game da batutuwan da suka jibanci nukiliyar kasar Iran.
Taron na ranar Asabar dai ya samu halartar mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi, da takwarar sa ta Amurka Wendy Sherman.
Tun dai a farkon watan Afirilun da ya gabata ne Amurka da kasashen dake goya mata baya suka bayyana amincewa, da aiwatar da karin yarjejeniyar da hukumar IAEA ta gabatar don gane da Nukiliyar kasar ta Iran, matakin da ya baiwa hukumar karin karfi bincikar wannan batu yadda ya kamata. Sai daga bisani Iran ta bayyana matakin a matsayin abin da sam bai dace ba, wanda kuma ke tattare da nuna bambanci.
Kasashe shida masu ruwa da tsaki game da wannnan batu, wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, da kuma kungiyar tarayyar Turai ta EU da ita kan ta Iran, sun cimma matsaya daya kan batun nukiliyar kasar ta Iran a ranar 2 ga watan Afirilun da ya gabata, matakin da ya zama tubalin inganta kokarin da ake yi, na cimma wata yajejeniya, kafin karshen watan Yunin dake tafe. Duka dai da nufin warware wannan batu daga dukkanin fannoni.
Sai dai da dama daga kasashen duniya na nuna matukar shakku game da yiwuwar hakan, ganin yadda shirin daukar matakan hadin gwiwa da Amurka ke goyon baya, ke sabawa ra'ayin kasar ta Iran. (Amina)