in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a dage wa'adin shawarwari kan batun nukiliya na Iran zuwa ranar 7 ga watan nan
2015-07-01 13:22:06 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Marie Harf ta bayyana jiya Talata cewar za a kara jinkarta wa'adin shawarwari game da batun nukiliyar kasar Iran zuwa ranar 7 ga watan nan, domin kara samun lokacin shawararin.

Madam Harf ta sanar da haka ne a shafinta na Twitter, inda ta ce, Iran da kuma kasashe shida da batun nukiliyar Iran ya shafa wadanda suka hada da Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma Jamus sun riga sun amince da wannan kuduri.

A baya an tsara cimma yarjejeniyar karshe game da batun nukiliyar ta Iran ce daga dukkan fannoni a ranar 30 ga watan jiya. Amma sabo da sarkakiyar da shawararin ke ciki, da kyar a iya warware wannan matsala cikin lokacin da aka tsara a baya. Ganin haka, bangarori daban daban da ke halartar shawarwarin suka tsai da kudurin cewa, ya kamata a kara wa'adin shawarwarin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China