Mr. Araqchi ya zanta da mataimakan ministocin kasashen da batun ya shafa har tsawon kwanaki uku a birnin Vienna na kasar Austria, bayan kuma komawarsa gida ne ya bayyana cewa sabanin dake tsakanin masu ruwa da tsaki ne ya haddasa rashin cimma matsaya game da yarjejeniyar karshe. Ya ce bisa amincewar bangarorin, idan har wani bangare bai amince da matsayar daya bangaren ba, za a soke matsayar daya bangaren a sake komawa farkon tattaunawar.
A farkon watan Afrilun shekarar nan ne kasar Iran, da kasashe shida da batun nukiliyarta ya shafa su fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana cimma ra'ayi guda kan aniyar shirin da ake yi na warware batun nukiliyar kasar. Kaza lika sun ambata cewa bangarorin da abin ya shafa za su dukufa, wajen cimma yarjejeniyar karshe kafin ranar 30 ga watan Yunin nan. (Maryam)