A yayin ganawar Wang Yi ya bayyana cewa, shawarwarin da aka dade ana yi ya shiga wani muhimmin mataki na karshe, saboda haka nauyin a bisa wuyan bangarori daban daban da abin ya shafa shi ne su yi kokarin cimma wata yarjejeniyar da ta shafi dukkan fannoni. Wang ya ce, kasar Sin na fatan bangarorin za su iya kawar da duk wani cikas domin cimma yarjejeniya mai adalci da daidaici. Kasar Sin ma na son ci gaba da taka rawarta a wanan fannin.
A nasa bangaren Javad Zarif ya bayyana cewa, kasar Iran ta yaba sosai ga taimakon da kasar Sin ta bayar wajen inganta shawarwari game da batun nukiliyar Iran, tare da fatan Sin za ta dauki matsayi mai adalci domin ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan wannan batun. Ya kara da cewa, kasarsa na kokarin ganin an cimma wata yarjejeniya a dukkan fannoni, tare da cire takunkumin da aka saka mata, tana kuma son yin mu'ammala sosai tare da Sin a wannan fanni. (Bilkisu)