Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta ce Sin ta yi matukar Allah wadai da kisan Hisham Barakat, babban mai shigar a kasar Masar.
Madam Hua ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labaru da ya gudana a ranar Talatar nan, tana mai nanata matsayin da Sin ke dauka na yaki da duk wani nau'in aiki irin na ta'addanci.
Hisham Barakat dai ya rasu ne sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai masa a ranar Litinin. (Amina)