Bisa labarin da jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta bayar a kan shafin Internet, an ce, wasu kungiyoyi masu goyon bayan tsohon shugaba Mubarak sun yi kira ga jama'a da su yi zanga-zanga a wannan rana. A yayin da kuma wasu mutane masu adawa da wadannan kungiyoyin suka yi fito na fito da 'yan sanda a wurare daban daban a kasar. Bisa labarin da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta bayar, an ce, mutane a kalla 18 sun mutu a sakamakon rikice-rikicen. A ciki, yawan mutanen da suka mutu sakamakon rikicin da aka samu a birnin Alkahira ya kai 11, ciki har da wani dan sanda. Haka kuma an samu mutanen da suka mutu a sakamakon rikice-rikicen da suka barke a birnin Alexandria, da jahohin Giza da Beheira.
Kana ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta bayyana cewa, mutane a kalla 38 sun ji rauni a sakamakon wadannan rikice-rikicen. Tuni dai ma'aikatar harkokin cikin gida ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an kama masu zanga-zanga kimanin 150. (Zainab)