in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta doke Najeriya a wasan kwallon tebur ta matasa
2015-03-18 10:22:39 cri
Dan wasan kwallon tebur Shady Magdy daga kasar Masar, ya doke takwaransa na Najeriya Onaolapo Ojo da maki 3-2, a wasan karshe na gasar matasa 'yan kasa da shekaru 21 da hukumar ITTF ta shirya.

Bayan kammalar gasar, Ojo wanda shi ke rike da kambin gasar, ya ce ya yi takaicin rasa damar kare kambin na sa. Ya ce ya koyi darasi daga wasan na wannan karo, zai kuma dauki matakan gyara a nan gaba.

A bangaren mata kuwa, Dina Meshref ce ta kare kambin da take rike da shi na gasar kwallon teburin, bayan da ta doke Yousra Helmy dukan su 'yan kasar Masar.

An dai gudanar da wannan gasa ne tsakanin ranekun 10 zuwa 14 ga watan nan na Maris, a zauren wasa na Molade Okoya-Thomas, wanda ke filin wasan Teslim Balogun dake birnin Ikkon jihar Lagos a tarayyar Najeriya. Gasar da 'yan wasa 81 daga kasashe 11 suka halarta.

Kuma wannan ne karo na 3 da Najeriya ta karbi bakuncin wannan wasa, gasar da ake rabawa wadanda suka samu nasara cikin ta kudi har dalar Amurka 46,000.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China