in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta dage shari'ar Morsi kan leken asiri
2015-02-16 14:54:04 cri

Kotun hukunta laifuffuka ta birnin Caire ta dage a ranar Lahadi da shari'ar tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi da wasu mutane goma mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi da ake zagi da laifin leken asiri, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA.

Morsi da wasu mutanen da ake tuhumar dai ana zarginsu da satar bayanan tsaro da na soja tare da kuma tsegunta su ga hukumomin leken asirin kasar Qatar da gidan talabijin na Al-Jazira dake da cibiya a birnin Doha. Shari'ar za ta iyar soma wa a ranar 28 ga watan Febrairu, domin baiwa masu kare wadannan mutane damar binciken takardun da suka shafi harkar, in ji MENA. Shari'ar wannan ranar Lahadi ita ce ta farko irin wannan dake da nasaba da leken asiri. Shugaban fadar Morsi, Ahmed Abdel Aatti tare da sakatarensa Ameen al Serafi na daga cikin mutanen da ake tuhuma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China