in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Masar ta kafe kan hukuncin kisa da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Morsi tun da fari
2015-06-17 13:59:45 cri
A jiya ne kotun hukunta manyan laifuffuka dake birnin Alkahira ta kasar Masar ta sanar da kafe kan hukuncin kisa da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi tun da fari .

Haka zalika kuma, kotun ta yanke wa Morsi hukuncin daurin rai da rai bisa zargin aikata leken asiri.

A shekarar 2012 ne, Morsi ya lashe zaben shugaban kasar Masar, wanda ya kasance shugaba na farko da jama'ar kasar suka zaba ta hanyar demokiradiya. Bayan da ya shafe shekara daya a kan kujerar shugabancin kasar, sojojin kasar suka yi masa juyin mulki sakamakon boren kin jin gwamnatinsa da jama'ar kasar suka yi. Daga bisani aka kama Morsi, aka kuma zarge shi da aikata laifuffuka da suka hada da tunzura jama'a su yi bore da sauransu.

Kafofin watsa labaru na kasar Masar sun yi nuni da cewa, bisa dokokin kasar Masar, duk da cewa, an kafe kan hukuncin kisa da aka yanke wa Morsi a wannan wata, Morsi da sauran mutanen da aka yanke musu hukunci suna da damar daukaka kara. Bayan da kotun daukaka kara ta saurari shari'ar, a karshe kotun kolin kasar za ta yanke wa Morsi hukuncin karshe. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China