Bayan kammala yiwa kamfanin kwaskwarima, ana sa ran zai rika samar da jiragen ruwa da ka iya daukar kayayyaki masu nauyin ton dubu 230 a kowace shekara, zai kuma zama kamfanin samar da jiragen ruwa mafi girma, dake da injiniyoyi mafiya yawa a dukkanin fadin nahiyar Afirka.
Kamfanin dillancin labaru na gabas ta tsakiya a Masar, ya bayyana cewa kammala wannan aiki, ya zamanintar da karfin kasar Masar a fannin samarwa, da kuma gudanar da gyare gyare ga jiragen ruwa.
Kamfanin cinikayyar jiragen ruwa na kasar Sin, wanda ke karkashin kamfanin CSSC ne dai ya jagoranci wannan aiki. An kuma fara gudanar da shi ne cikin watan Janairun shekarar 2011, ya kuma lashe jimillar kudi har kimanin dala miliyan 200. Kaza lika an aiwatar da kwarkwarima ga wannan kamfani ne bisa mizanin sahihanci na kasar Sin.
Bikin kammala aikin ya samu halartar shugaban kasar Masar Abdel Fatah Al Sisi, da firaministan kasar Ibrahim Mahlab.
Rusasshiyar tarayyar soviet ce ta kafa wannan kamfani, a shekaru 60 na karnin da ya gabata. (Fatima)