Mahlab ya bayyana cewa, masu zuba jari daga kasashe daban daban sun daddale yarjejeniyoyin tattara kudi da yawansu ya kai dala biliyan 18.6 tare da bangaren kasar Masar, kana kungiyoyin bada lamuni na kasa da kasa ma sun daddale yarjejeniyar bada rancen kudi ga ma'aikatar hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Masar da yawansu ya kai kimanin biliyan 5.2. Haka kuma, kasashen Saudiyya, Kuwait, hadaddiyar daular Larabawa da Oman sun jaddada cewa, za su cika alkawarinsu na samar da taimakon kudi na dala biliyan 12 ga kasar Masar. Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na MENA na kasar Masar ya bayar, an ce, an cimma yarjejeniyoyin zuba jari tare da takardun fahimtar juna da yawan kudinsu ya zarce dala biliyan 92 a yayin wannan taron.
Mahlab shi ma ya nuna godiya ga gwamnatoci da masu zuba jari na kasa da kasa a cikin jawabinsa na rufe taron, kana ya yi nuni da cewa, kasashe daban daban na yankin da kasar ke ciki da sauran yankunan duniya sun halarci taron raya tattalin arzikin kasar Masar, wannan ya alamanta cewa, kasar Masar ta hau turbar samun bunkasuwa mai dacewa. (Zainab)