in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar: Kotu ta kafe kan hukuncin da ta yanke wa Mubarak
2015-05-10 16:39:14 cri

Wata kotun majistare dake zaman ta a birnin Alkahira na kasar Masar, ta sanar kafewar ta, kan hukuncin da ta yanke wa tsohon shugaban kasar Mohammed Hosni Mubarak, bisa samun sa da laifin karkatar da wasu kudaden gwamnatin kasar domin amfanin kashin kan sa.

Hukuncin kotun dai ya tanaja zaman kaso na shekaru 3 ga tsohon shugaban kasar, yayin da kuma aka rage tsawon shekaru da za a tsare 'ya'yansa maza su 2, daga shekaru 4 zuwa shekaru 3.

A ranar 21 ga watan Mayun shekarar bara ne kotun ta yanke wa Mubarak hukuncin daurin na shekaru 3, da kuma 'ya'yan nasa su 2, wadanda a wancan lokaci aka zartaswa hukuncin daurin shekaru 4 bisa laifin barnata dukiyar gwamnati.

An dai zargi mutanen uku da barnata kudade, da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 14, kudaden da aka ware domin yiwa fadar shugaban kasa kwaskwarima.

A kuma ranar 13 ga watan Janairun bana ne wata kotun kasar ta karbi karar da Mubarak da 'ya'yan nasa su 2 suka daukaka, ta kuma bayyana fara sauraron shari'ar ta su. A kuma ranar 25 ga watan Janairun ne aka saki 'ya'yan nasa, duk da cewa ana tuhumar su da laifin karkatar da wasu kudaden gwamnati domin amfanin kashin kansu, da kuma wani laifin mai alaka da gudanar da haramtacciyar cinikayya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China