A yayin ganawarsu, Mr. Gao ya bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali da kuma goyon bayan kasar Masar wajen raya tattalin arzikin kasar, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.
A nasa bangare, Abdelfattah al Sisi ya bayyana fatan alheri ga shugaba Xi Jinping, da nuna godiya sosai ga halartar ministan harkokin kasuwanci na Sin Gao Hucheng a wannan babban taron raya tattalin arzikin kasar Masar, tare da ba da jawabi a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin.
Haka kuma, Abdelfattah al Sisi na maraba da halartar kamfanonin kasar Sin cikin ayyukan gina kasar Masar, kuma yana fatan karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan aikin gina kayayyakin more rayuwa da dai sauransu. (Maryam)