Sanarwar da kwamitin sulhun MDD ya fitar, ta yi tir da hare-hare na ta'addanci, tare da jaddada aniyar tallfawa yaki da dukkanin ayyukan da suka jibanci tada kayar baya.
Sanarwar ta kara da cewa ya zama wajibi a gaggauta hukunta wadanda suke da hannu cikin aikata wannan ta'asa, da masu tallafa musu. Kaza lika sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin dake wuyansu na aiwatar da dokokin kasa da kasa, da kuma ka'idojin MDD bisa wannan batu, tare da yin hadin gwiwa cikin himma da kwazo, tare da gwamnatin kasar Masar a wannan fanni.
Kwamitin sulhun MDD ya kuma jaddada cewa, ya zama wajibi kasashen duniya su dauki matakan yaki da ta'addanci bisa dokokin kasa da kasa.
A nasa bangare, babban magatakardar MDD cewa ya yi, hare-haren da aka kai lardin na Sinai ta Arewa dake kasar Masar abun takaici ne matuka. Cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar Mr. Ban ya kuma bayyana juyayinsa ga iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da rayukansu. (Maryam)