A safiyar ranar Litinin 16 ga wata, rundunar sojan ikasar Masar ta sanar da cewa, a wannan rana Kasar ta kai harin jirgin sama kan sansanonin wani sansanin kungiyar IS dake Libya da niyyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Masar, tare da yanke hukunci ga kungiyar ta'addanci da 'yan ta'adda, wadanda suka gudanar da danyun ayyuka a Masar da kasashen waje.
Bayan haka, sanarwar ta kara da cewa, an kai wannan hari ne a kan sansanin sansanoni da wuraren horaswa da dakin gidan adana makamai na kungiyar IS da ke Libya. An ce, an sami babbar nasara a wannan karo, kuma sojojin saman da suka gudanar da wannan aiki tuni suka koma gida.