in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Masar za ta gina wani sabon babban birninta a gabashin Alkahira
2015-03-15 09:43:19 cri

A ran 13 ga wata da dare, malam Mostafa Madbouly, ministan kula da harkokin samar da wuraren kwana na kasar Masar ya sanar da shirin gina wani sabon babban birnin kasar a gabashin Alkahira, wanda zai iya daukar mutane miliyan 5.

Malam Mostafa Madbouly ya sanar da wannan shiri ne a yayin taron bunkasa tattalin arzikin kasar Masar da aka shirya a birnin Sharm el Sheikh dake kudancin tsibirin Sinai.

Bisa bayanin da aka bayar a jaridar All-ahram, an ce, sabon babban birnin kasar Masar zai kasance a tsakanin Alkahira da kogin Suez, fadinsa zai kai murabba'in kilomita dari 7. Bugu da kari, yankin dake kunshe da wata sabuwar fadar shugaban kasar da galibin hukumomin gwamnati da gidajen jakadancin kasashen duniya dake kasar Masar zai kai eka dubu 1. Sannan, za a samar da gidajen kwana miliyan 1 da dubu dari 1 wadanda za su iya daukar mazauna miliyan 5.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, za a kwashe shekaru 5 zuwa 7 wajen kokarin kamala matakin farko na shirin, kuma za a kashe dalar Amurka biliyan 45. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China