in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ya yi allah wadai da kisan 'yan kasar Masar
2015-02-16 15:08:11 cri
Jiya Lahadi 15 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa, inda ya yi allah wadai da babbar murya dangane da kisan 'yan kasar Masar na darikar Copt guda 21 da rashen kungiyar IS dake kasar Libya ya yi a kwanakin baya, haka kuma kwamitin ya jaddada aniyarsa ta murkushe kungiyar IS.

Sa'an nan kuma shugaban kasar Masar Abdelfattah al Sisi ya sanar a ran 15 ga wata da dare cewa, kasarsa za ta dauki matakai yadda ya kamata dangane da lamarin kisan 'yan kasar da kungiyar IS ta yi garkuwa da su.

Kaza lika, fadar shugaban kasar ta Masar ta fidda wata sanarwa, inda ta nuna juyayi dangane da kashe wadannan mutane 'yan kasar guda 21 a kasar Libya, tare da ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 7 a duk fadin kasar.

A wannan rana, rashen kungiyar IS dake kasar Libya ya gabatar da wani bidiyo a shafin intanet dake nuna dakurun IS fuska boye suna kashe 'yan kasar Masar na darikar Copt guda 21. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China