A farkon watan nan da muke ciki, gwamnatin kasar Mali da wasu kungiyoyin siyasa da sojoji guda shida dake arewacin kasar suka kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Algiers na kasar Algeria, karkashin yarjejeniyar an amince da samar da sulhu a tsakanin kabilun kasar Mali bisa tushen kiyaye dunkulewa da kuma cikakken yankunan kasa, kana ya kamata a girmama al'adun kabilu daban daban dake kasar, a kuma hada kai domin yaki da ayyukan ta'addanci, haka kuma gwamnatin kasar za ta kara samar da kasafin kudi ga yankin arewacin kasar.
Dangane hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Jumma'a cewa, kasar Sin na yin kira ga bangarori daban dabban na kasar Mali da su kiyaye dunkulewa da kuma cikakken yankunan kasar.
Kasar Sin na kuma fatan za a hanzarta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba a kasar. (Maryam)