Cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, Ban Ki-moon ya ce kulla yarjejeniyar babban mataki ne na samun ci gaba a aikin shimfida zaman lafiya a duk fadin kasar ta Mali.
Ya ce burin siyasa na bangarori daban daban da batun ya shafa na da muhimmiyar ma'ana wajen cimma manufar zaman lafiya na dindindin a kasar. Don haka ya kamata bangarorin su ci gaba da dukufa, domin lalubo hanyoyin da suka dace na warware matsalar kasar daga tushe.
Daga nan sai ya bayyana burin MDD na ci gaba da goyon bayan al'ummar kasar ta Mali, wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma yadda ya kamata, ta yadda za a iya kai ga wanzar da zaman lafiya, da tsaro, da adalci da kuma ci gaba a kasar. (Maryam)