Kwamitin kuma ta yi kira ga gwamnatin Mali da ta yi bincike kan wannan al'amari tun da wuri tare da gurfanar da wadanda suka aikata shi a gaban kotu. Kwamitin ya nanata cewa, ya kamata a dakile duk wani aikin ta'addanci bisa kundin tsarin mulkin MDD, ban da hakan, ya nanata wajibcin nuna goyon bayan kokarin da tawagar musamman da MDD ta tura ma Mali ta yi don taimakawa mahukunta da jama'ar kasar wajen wanzar da zaman lafiya mai karko.
A safiyar ranar 7 ga wata ne, aka kai hari a wani dakin cin abinci dake tsakiyar birnin Bamako, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, yayin da wasu da dama suka ji rauni. 'Yan sandan kasar Mali sun bayyana cewa, cikin wadanan suka rasu, akwai wani dan Faransa da dan Belgium, da 'yan kasar Mali uku. Yanzu an cafke mutane biyu da aka zargin da alaka da lamari, kuma ana ci gaba da bincike. (Amina)