in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta bi hadaddiyar sanarwa kan batun nukiliyar Iran, in ji shugaban kasar
2015-04-04 16:59:42 cri
Jiya Jumma'a 3 ga wata, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ba da jawabi ta gidan talabijin, inda ya taya murnar cimma hadaddiyar sanarwa kan batun nukiliyar kasar a tsakanin kasashen shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da kasar Iran da kuma kungiyar tarayyar kasashen Turai EU, ya kuma bayyana cewa, kasar Iran za ta bi sharudan da sanarwar ta tanada.

Bugu da kari, Mr. Rouhani ya ce, kasar Iran za ta cimma alkawarinta da abin ya shafa da kuma daukar alhakinta yadda ya kamata, idan bangarorin da abin ya shafa suka bi sharadun da suka cimma ra'ayi daya a yayin shawarwarin yadda ya kamata. Ya kuma kara da cewa, hanyar da hadaddiyar sanarwa take bi ta dace da halin da ake ciki yanzu, ta kuma dace da moriyar kasar Iran, lamarin da ya kasance babban sakamakon da kasar Iran ta samu, kasar Iran ta nuna kyakkyawan fatanta a yayin shawarwarin, haka kuma, za ta ci gaba da neman hanyoyin da za su dace da shawarwarin da bangarorin da abin ya shafa.

Kaza kila, Mr. Rouhani ya bayyana cewa, za a dakatar da dukkanin takunkumin da aka kakaba wa kasar Iran, da zarar an kulla cikakkiyar yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar Iran, sa'an nan kuma, kasar Iran za ta ci gaba da shirinta kan karfafa sinadarin uranium a kasar, ta yadda za ta iya maimaita fasahohinta kan aikin. Wannan ya nuna cewa, aikin karfafa sinadarin uranium da kasar Iran ta yi shi ne na zaman lafiya, wanda ba zai kasance ba wata barazana ga sauran kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China