in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran da Afghanistan za su hada gwiwa wajen yaki da 'yan ta'adda
2015-04-20 09:59:35 cri
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce, kasarsa za ta yi hadin gwiwa da kasar Afghanistan wajen yaki da 'yan ta'adda.

Gidan talebijin na kasar Iran ya nuna Rouhani, wanda ke ganawa da takwaransa na kasar Afghanistan Mohammad Ashraf Ghani, a birnin Tehran a jiya Lahadi, na cewa, kasashen biyu sun amince su yi amfani da bayanan siri da kowannen su ya samu game da 'yan ta'adda, ko masu tsattsauran ra'ayi a iyakokin kasashen biyu, kana su yi amfani da hakan wajen daukar matakan da suka dace, da zarar sun amince da aiwatar da hakan.

Rouhani ya kuma bayyana cewa, kasashen biyu za su daukaka matsayin hadin gwiwa game da samun bayanan sirri, da na harkokin tsaro tsakaninsu, don yaki da laifukan fasa kwaurin miyagun kwayoyi a ketaren kasashen. Musamman kasancewar Afghanistan babbar kasa a fannin safarar tabar wiwi, da hodar ibilis, inda ake safarar akasarin wadannan kwayoyi daga kasar zuwa sauran kasashen duniya ta hanyar iyakokin Iran.

A nasa bangare kuma, shugaban Ghani ya ce, yanzu haka, dukkanin yankin Gabas ta Tsakiya na fuskantar babban kalubale daga 'yan ta'adda, don haka ya dace kasashen biyu su hada kai don yaki da kungiyar IS da sauran kungiyoyi makamantanta.

A wani ci gaban kuma, shugabannin kasashen biyu sun rattaba hannu kan takardar fahimtar juna a fannoni daban daban.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaba Ghani ya kai ziyara kasar Iran, tun bayan da ya dare karagar mulki a cikin watan Satumbar bara. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China