Wannan ne albishir mai kyau daga kasar ta Iran da hukumar IAEA ta samu a 'yan lokacin nan.Wannan ne ra'ayi mai yakini da kasar Iran ta bayar ga hukumar IAEA. Amma ya zuwa yYanzu ba a san ko ayyuka na'urori ba na samar da makamashin nukiliya ba sun hada da ayyukan soja ko a'a.
A cikin shirin ayyukan hadin gwiwa da kasar Amurka ta gabatar a farkon wannan wata, an ce, kasar Iran za ta dauki jerin wasu matakai don kawar da shakkun da hukumar IAEA ta ke yi mata kan yadda take gudanar da game da shirinta na makamashin nukiliya domin aikin soja.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, kasar Iran ta ki amincewa da bukatar sauran bangarori da su bukaci shigata binciken ayyukan na'urorinta na soja ko da sansaninta na harbar makamai masu linzami na kasar Iran.
A cikin shawarwari na sabon zagaye kan batun nukiliya na kasar Iran da aka kammala a birnin Vienna a kwanakin baya, bangarori daban daban sun shirya daddalekaddamar da tsara yarjejeniyar karshe game dakan batun a daga dukkan fannoni. Amma ba su bayyana fayyace ko akwai ci gaban da aka samu kan batun yin bincike kan ayyukan na'urorin soja na kasar Iran ba. (Zainab)