in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka: Za a aiwatar da yarjejeniyar batun nukiliyar Iran
2015-04-07 10:08:37 cri
Ministan ma'aikatar harkokin makamashin kasar Amurka Ernest Moniz, ya bayyana cewa ba a tsara wa'adin aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran ba, tsarin da ake fatan ya dore har abada.

Moniz ya bayyana hakan ne ga taron manema labaru da fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta gudanar a ranar 6 ga wata. Ya ce yarjejeniyar za ta yanke dukkan hanyoyin samar da makaman nukiliya ga kasar Iran, da bincike dukkan ayyukan nukiliya na kasar Iran a kowane lokaci, domin tabbatar da ganin Iran din ta yi biyayya ga yajejeniyar cikin dogon lokaci.

Moniz ya kuma musunta rade-radin da ake yi cewa wai Amurka da Iran ba su cimma daidaito game da abubuwan dake kunshe cikin shirin warware batun nukiliyar Iran ba, wato bangarorin biyu sun maida hankali ne kawai ga fannoni na daban yayin da suke tattaunawa kan yarjejeniyar.

Game da hakan Mr. Moniz ya ce, bayanan da bangarorin biyu suka yi bai saba wa yarjejeniyar da aka daddale ba.

A daya hannun kuma kakakin fadar shugaban kasar Amurka Josh Ernest, ya bayyana cewa ba za a soke dukkan takunkumin da aka sanyawa kasar Iran nan take ba bayan daddale yarjejeniyar nukiliyar kasar a dukkanin fannnoni, domin hakan ba zai dace da moriyar kasa da kasa ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China