in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na maraba da cimma ra'ayi guda game da batun nukiliyar Iran
2015-04-03 21:14:24 cri
A yau Jumma'a ne bayan kasashen nan shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da ita kanta kasar Iran sun fidda hadaddiyar sanarwa game da shawarwarin da suke gudanarwa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasar Sin na maraba da ra'ayin da bangarorin suka cimma kan batun nukiliyar kasar Iran, matakin da ya ce kyakkyawan labari ne ga kasashen duniya. Ya ce kasashen shida da wannan batu ya shafa da kasar Iran, sun dukufa wajen cimma ra'ayi guda, wanda kuma ya kasance babban tushe na cimma cikakkiyar yarjejeniya kan batun a nan gaba.

Wang Yi ya kuma kara da cewa, ana bukatar ci gaba da yin shawarwari domin cimma cikakkiyar yarjejeniya, kana kasar Sin na fatan za a yi amfani da sakamako mai kyau da aka cimma, wajen kawar da sabanin dake tsakanin bangarorin da abin ya shafa, ta yadda za a iya ciyar da yukurin da ake yi gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China