in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban koli na Iran nadari-dari game da shawarwarin nukiliyar kasar
2015-04-10 15:57:44 cri
Shugaban majalissar koli ta addini a kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya bayyana dari-dari game da sabon ci gaba da aka samu don gane da shawarwari kan batun nukiliyar kasar.

Da yake bayyana matsayarsa game da wannan batu a ranar 9 ga wata a birnin Tehren, Khamenei ya ce sabon ci gaban da aka samu a yayin shawarwarin ba zai tabbatar da daddale yarjejeniya tsakanin bangarori daban-daban ba, kuma ba a kai ga kawo karshen shawarwarin ba.

Ya nuna damuwarsa ga yiwuwar Iran za ta fada tarkon da kasashen yammacin duniya suka dana mata bisa wasu kananan abubuwa. A daya bangaren kuma ya sake nanata cewa muddin Iran ta yi la'akari da cikakken bayani filla-filla, za ta gano alkiblar matakan da za a dauka cikin shawarwarin.

Game da batun shirin matakan da za a dauka wanda Amurka ta gabatar, Khamenei ya ce shirin ya murde gaskiya, kuma ba za a yi amfani da shi a matsayin ka'idar da za a bi a fannin neman ci gaban shawarwarin ba.

Khamenei ya kara da cewa, a lokacin da bangarori daban daban ke daddale yarjejeniya game da batun nukiliyar kasar, ya zama dole kasashen yammacin duniya su soke takunkumin tattalin arziki, da na hada-hadar kudi da suka kakaba wa Iran.

Wannan shi ne karo na farko da Khamenei ya furta ra'ayinsa, tun bayan da bangarori daban-daban suka cimma matsaya guda, game da batun nukiliyar kasar ta Iran.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China