Ya kuma kara da cewa, kasar Iran na tsayawa tsayin daka wajen kin amincewa da bincike cikin sansanonin sojin kasar, haka kuma, kasar Iran ba za ta amince da bangarorin da shawarwarin batun nukiliyar kasar Iran ya shafa su sa ido kan harkokin makamai masu linzami na kasar Iran ba.
Mr. Araqchi ya bayyana haka ne, bayan wani bayani kan shirin da kasar Amurka ta fidda kwanan baya, inda cikin shirin, kasar Amurka ta ce, kasar Iran ta amince da daukar duk irin matakan da aka bukace ta, domin bayyana cewa, ba ta da shirin yin amfani da makamashin nukiliyar kasa cikin harkokin soja. (Maryam)