Abbas Akhondi ya kara da cewa yanzu haka hidimomin kamfanonin zirga-zirgar jiragen saman fasinjan kasar ta Iran ba sa iya biyan bukatun kasar, a sabili da haka ya ce kamata ya yi a kara zuba jari a wannan fanni. A sa'i daya kuma, ya ce kasar za ta rage yawan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama a kasar, a wani yunkuri na kara karfin kamfanin jirgin sama mallakar gwamnatin kasar.
Bayan da kasashen duniya suka kakaba mata takunkumi, an kayyade Iran wajen sayen sabbin jiragen saman fasinja, wanda hakan ya sa jiragen saman ta suka zamo tsofaffi kwarai.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, ta kan sayi kayayyakin jiragen sama a kasuwanni bisa farashi mai tsada sosai, inda a wasu lokutan akan yi amfani da sassan wasu jigaren domin gyara wadanda ake amfani da su. A sakamakon haka, hadurran jiragen sama suka karu a kasar ta Iran cikin 'yan shekarun baya bayan nan. (Fatima)