in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban masu halartar shawarwarin batun nukiliya na Iran sun cimma shirin warware batun
2015-04-03 11:20:03 cri
Kasashe shida da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa wato Sin, Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, tare da kungiyar EU da kuma kasar Iran sun cimma shirin warware batun a ranar alhamis, ta haka aka aza tubali wajen cimma yarjejeniyar warware batun a dukkan fannoni.

Babban wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Federica Mogherini da minister harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif sun gabatar da hadaddiyar sanarwa a birnin Lausanne dake kasar Switzerland.

A wannan ranacikin sanarwar, an ce, bangarori daban daban da abin ya shafa sun cimma daidaito kan kayyade ayyukan samar da makamanyin amfani da makamashin nukiliya da karfin tace sinadarin Uranium da ajiye abubuwan masu alaka da nukiliya a kasar Iran, kana sun gabatar da shirin sa kaimi ga kasa da kasa da su taimakawa kasar Iran wajen yin amfani da fasahohin nukiliya cikin lumana.

Haka kuma sun yi alkawarin dakatar da takunkumin da Amurka da kungiyar EU suka yiwa kasar Iran a fannin tattalin arziki da kuma kudurin kwamitin sulhu na MDD game da takunkumin da aka yi matawa kasar.

Minista Zarif da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry sun gudanar da taron manema labaru bayan da aka gabatar da sanarwar. Zarif ya bayyana cewa, matakin da kasar Iran ta taka dauka ya shaidawa bangarorin da suka zarge takasashen da suka tsoma baki cikin harkarta ta sarrafa sinadarin Uranium cewa, shirin nukiliya na kasar Iran yana da nufin tabbatar da zaman lafiya.

Mr Kerry ya bayyana wa 'yan jarida cewa, shirin da bangarori daban daban da abin ya shafa suka cimma a birnin Lausanne yana da babbar ma'ana, ganin warware matsalar nukiliya ta kasar Iran za ta taimakawa wajen kokarin kyautata dangantakar dake tsakanin Iran da Amurka.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta kakakinsa a ranar 2 ga wata, inda ya taya murnar cimma shirin warware batun nukiliya na kasar Iran a wannan rana, ya ce shirin ya aza tubali ga cimma yarjejeniyar warware matsalar a dukkan fannoni kafin ranar 30 ga watan Yuni na bana.

Sanarwar ta kara da cewa, cimma yarjejeniyar warware matsalar nukiliya ta Iran a dukkan fannoni da ake neman cimma za ta kasance abin da ya shirya share fagen kokarin kayyade ayyukan nukiliya da soka soke takunkumin da aka yiwa kasar Iran, kana za ta girmama bukatu da hakkin kasar Iran, da shaida wa kasa da kasa cewa aka ana gudanar da dukkan ayyuka masu alaka da n nukiliya na a kasar Iran domin tabbatar da zaman lafiya a kasar kawai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China