Wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane a kalla 25, sakamkon wani Bam da ya tayar a wani masallaci dake birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. Baya ga wadanda suka rasa rayukan su a harin na ranar Asabar, rahotanni sun ce wasu karin mutanen 28 sun samu raunuka.
'Yan sandan jihar ta Borno sun shaidawa manema labaru cewa, dan kunar bakin waken ya tashi Bam din dake jikin sa ne da misali karfe 3 da rabi na yamma, a wani masallaci dake dab da kasuwar "Monday market". A daya hannun kuma, gwamna Kashem Shattima na jihar ta Borno ya ce masu ceto sun isa wurin da lamarin ya faru domin bada agajin jin kai, yayin da ake ci gaba da bincike game da faruwar lamarin.
Babu dai wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Amina)