Mista Han ya shaidawa manema labaru cewa sun samu tattaunawa tare da cimma wata yarjejeniya kan batutuwan da ke nasaba da huldar dangantaka da moriyar kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Sin a shirye take na ta yi aiki tukuru tare da sabuwar gwamnatin Najeriya domin karfafa huldar danganataka tsakanin kasashen biyu.
Manzon musamman na kasar Sin, ya samu kuma ganawa tare da manyan jami'an Najeriya domin maida hankali kan dangantaka a fannonin gine gine, wutar lantarki da noma, da fannonin da shugaba Buhari ke fatan ganin an kara karfafa dangantaka ta moriyar juna.
Kasuwanci tsakanin Sin da Najeriya ya cimma dalar Amurka biliyan 18.1 a shekarar da ta gabata. Kuma kasar Najeriya ita ce zangon kasuwanci na biyu ga kasar Sin a nahiyar Afrika.
Sannan a yayin bikin rantsuwar kama aiki da aka shirya a ranar Jumma'a, sabon shugaban Najeriya Muhammadu Bahari ya yi alkawarin gudanar da aikin shugabancinsa yadda ya kamata da kare 'yanci a fadin kasar Najeriya, hada kan 'yan Najeriya, samar da wadata da kuma ci gaban Najeriya. Kusan Shugabannin Afrika goma da na sauran nahiyoyi suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya ciki har da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika a wannan karo.
A cikin jawabin da ya gabatar, mista Buhari ya bayyana cewa rundunar sojojin Najriya za ta aike da hedkwatarta a Maiduguri, hedkwatar jihar Borno dake arewacin Najeriya, kuma ta tsaya har sai an ci nasara kan kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)