Manzon musamman na shugaban Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Nijeriya
2015-05-26 19:54:30
cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau Talata cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Nijeriya ta yi wa kasar Sin, ministan harkokin noma na kasar Sin Han Changfu zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari wanda za a yi a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping. (Maryam)