A cewar ministar yada labarun kasar Patricia Akwashiki, shugaba Jonathan ya yanke shawarar mika ragamar mulkin kwana guda, kafin ranar da aka saba gudanar da bikin.
Akwashiki ta ce bisa sabon tsarin, za a gudanar da bikin mika mulkin ne a daren ranar 28 ga watan na Mayu, yayin liyafar cin abincin dare da fadar shugaban kasar za ta shirya, wanda hakan zai baiwa sabuwar gwamnatin damar gudanar da shagulgunan ranar dimokaradiyya, da rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu.
Bisa tsarin na yanzu, mai yiwuwa shugaba Jonathan ba zai halarci bikin rantsuwar da Muhammadu Buhari zai yi a ranar ta 29 ga wata ba.
Yanzu haka dai kwamitin da shugaban mai barin gado ya kafa, domin shirya mika mulkin karkashin jagorancin mataimakinsa Namadi Sambo ya fara aiki gadangadan. A daya hannun kuma, an bayyana sunan sakataren gwamnatin kasar Pius Anyim, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin gudanarwa na bikin rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a ranar 29 ga watan na Mayu. (Saminu Hassan)