Kakakin rundunar 'yan sandan Magaji Majiya ya sanar wa manema labarai Alhamis din nan cewa, an kame wadanda ake zargin ne a sassa daban daban na jihar, da aika abin da ya saba wa ka'idojin zabe na son tada zaune tsaye da kwace akwatunan zaben.
Malam Magaji Majiya ya ce, wadansun su ma an same su dauke da makamai, kamar su kwari da baka, wukake, takubba, sanduna da adda, sai dai ya jinjina wa al'ummar jihar bisa ga hadin kan da suka bayar ga hukumar 'yan sandan a lokacin zaben, abin da ya sa aka samu nasarar kammala zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa, su ma 'yan sanda a nasu bangaren sun nuna kwarewarsu na aiki matuka wajen tabbatar da an bi doka da oda yadda tsarin mulki ya tanada musu a lokacin zaben.
Daga nan sai ya yi kira ga daukacin 'yan Nigeriya musamman matasa da su yi taka tsantsan a kan yadda suke nuna murnarsu ta nasarar da Muhammadu Buhari ya yi domin kauce wa wassu tsautsayi. (Fatimah)