Haka kuma yayi alkawarin dunkulalliyar kasa, nagartatta tare da hada kan al'ummar ta, zaman lafiyar ta da cigaban ta a matsayin mafi yawan al'umma a daukacin nahiyar Afrika.
Rantsuwar kama aikin dai da babban mai shari'a na kasa Mahmoud Mohammed ya tabbatar da hakan a gaban dandazon al'ummar kasa da suka hada da abokan arzikin kasar na kasashen waje da suka hallara a babban filin eagle dake Abuja dandalin bikin rantsarwar.
Da yake magana a bikin liyafar jajibirin a daren jiya alhamis Shugaban kasa mai barin ado Goodluck Jonathan yayi kira ga sabuwar gwamnati mai kamawa data aiwatar da ayyuka da shirye shirye da zasu inganta hadin kan kasa da cigaban ta cikin sauri.(Fatimah Jibril)