in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa dokar hana fita a garin Maiduguri dake arewacin Najeriya
2015-05-14 19:58:48 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, hukumomin soja sun sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar da ke fama da rikicin Boko Haram.

Wata sanarwar da hedkwatar rundunar sojojin kasar ta bayar ta bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne sakamkon harin da wasu masu dauke da makamai da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka yi yunkurin kaiwa a garin na Maiduguri a ranar Laraba.

Bugu da kari, sanarwar ta bukaci mazauna garin na Maiduguri da su baiwa jami'an tsaro dukkan hadin kan da ya dace a kokarin da suke yi na kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

An ji karar harbe-harbe da abubuwan fashewa a sassa daban-daban na birnin a ranar Laraba, kafin daga bisani jami'an tsaro su killace wurin.

Bayanai na cewa, yanzu dai al'amura sun daidaita sai dai babu wani bayani daga jami'an tsaron game da asarar rayuka ko jikkata sakamakon wannan arangama. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China