A cewar kakakin hukumar Mitchell Ofoyeju, NDLEA za ta gabatar da Kashamu gaban kotu a ranar Litinin, domin neman takardar umarnin kotun, na mika shi ga kasar ta Amurka. Hakan dai a cewar Mr. Ofoyeju mataki ne da ya dace da dokokin Najeriya.
Sai dai a nasa bangare Sanata Kashamu ya zargi abokin hamayyarsa a siyasance, kuma jigo a jam'iyyarsu ta PDP Olabode George, da kulla masa makarkashiya. Ya ce uwargidan George wadda kuma ita ce babbar darakta a hukumar ta NDLEA, ita ce ke jagorantar wannan shiri na mika shi Amurka, duk kuwa da a cewarsa babban mai shari'ar kasar, kuma ministan shari'a ya hana NDLEAn daukar wannan mataki.
Kashamu ya kara da cewa akwai wata kara da ya shigar gaban kuliya, wadda kotu za ta yanke hukunci kanta a ranar Laraba, don haka ya bukaci hukumar ta NDLEA da ta dakatar da daukar wani mataki a kansa, har sai waccan kotu ta yanke nata hukunci. Kaza lika ya yi kira ga Amurka da ta yi watsi da wannan batu, duba da cewa cike yake da tufuma maras tushe. (Saminu Hassan)