Kamfanin gina layin dogo na CRCC na kasar Sin ya shafe shakara daya wajen gina tashar, kuma gwamnan jihar Lagos Babatunda Fashola da zai bar gado a ran 29 ga watan da muke ciki ya halarci bikin kammala gina wannan tashar samar da wutar lantarki, inda ya latsa maballin tashar da kansa.
A sassa da dama na Najeriya ana amfani da na'urorin samar da wutar lantarki masu aiki da man dizal domin samar da wutar lantarki da makamashi, amma saboda karancin mai da ake fama da shi a 'yan shekarun nan, wasu na'urorin samar da wutar lantarki ba sa aiki yadda ya kamata, wannan ya sa a kan fama da karancin wutar lantarki a kullum. (Maryam)