in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar raya masana'antu ta MDD ta kafa ofishin zuba jari na farko a Abuja
2015-04-30 10:25:42 cri

Hukumar raya masana'antu ta MDD (UNIDO), ta kafa wani sabon ofishi a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, wanda zai lura da harkokin zuba jari a mataki na kasa da kasa, tare da yada ayyukan kimiyya fasahohi mai lakabin ITPO, ofishin da zai kasance irin sa na farko da hukumar ta kafa a yankin kudu da Sahara.

Ministan masana'antu da cinikayya da harkokin zuba jari Olusegun Aganga a Najeriyar ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, kafa wannan ofishi ya nuna imanin da UNIDO ke da shi ga batun raya tattalin arzikin Najeriya yadda ya kamata. Ya ce, burin da wannan ofishi ke da aniyar cimmawa a dogon lokaci shi ne sa kaimi ga bunkasuwar masana'antu a kasar, tare da samar da guraben aikin yi, kana da sa kaimi ga ci gaban masana'antu a Najeriya da kasashen mambobin ECOWAS.

Hukumar UNIDO wadda ke karkashin sashi na musamman na MDD, na da muradin karfafa hadin gwiwa tsakaninta da mambobin majalisar sama da 170, domin inganta bunkasuwar masana'antu, da kuma samun bunkasuwa mai dorewa a kasashe masu tasowa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China