A kalla yara da manya kusan dubu daya ne suka samu binciken lafiya da magunguna kyauta da suka hada da binciken idanu da rarraba tabarau na kara gani, binciken lafiya da ba da jinya kyauta, tare da kuma binciken cutar cancer, hawan jini, yawan suga cikin jini da sauransu.
Siju Iluyomade na kungiyar Arise Women ya bayyana cewa wadannan ayyukan binciken lafiya da bada magunguna kyauta ana yinsu ne domin taimakawa al'ummomin da ba su da kudi zuwa asibiti idan suna fama da cutar suga ko ta hawan jini.
Mista Iluyomade ya bayyana cewa ayyukan kungiyarsa na da manufar bunkasa aikin bada jinya ta rigakafi tun daga tushe.
Mista Adebayo Olasubomi, wani mauzauni da ya samu gajiyar wannan aiki, ya bayyana cewa wadannan ayyuka na bada jinya kyauta za su karfafa kiwon lafiyar mazauna jihar, domin yawancinsu mutane ne da ba su da karfin ganin likita. (Maman Ada)