Yayin ganawar tasu, jakada Gu ya bayyanawa sarkin na Kano cewa dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya na kara bunkasuwa a 'yan shekarun baya bayan nan, kuma mu'ammala tsakanin jama'ar sassan biyu ta samu babban ci gaba. Daga nan sai Mr. Gu ya bayyana matukar godiyarsa ga goyon bayan da mai martaba sarkin Kano ke nunawa, wajen dorewar mu'ammala tsakanin bangarorin biyu.
Ya ce a daidai wannan lokaci na cika shekaru 10 da kafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, Sin na fatan ci gaba da samun zarafin zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Najeriya a fannoni daban-daban, ciki hadda tsakanin gwamnatoci da sauransu, ta yadda za a daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa matsayi na gaba.
A nasa bangare Sarkin na Kano jinjinawa hadin gwiwar sassan biyu ya yi, musamman ganin yadda hakan ke haifar da alfanu wajen raya tattalin arzikin jihar Kano. Kaza lika ya yaba da irin ci gaban da Sin take samu, tare kuma da fatan kasar ta Sin za ta kara zuba jari a jiharsa. Baya ga batun kara hadin gwiwa, da ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Amina)