in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kara gano makamai a garin Baga
2015-02-23 16:47:49 cri

Sojojin Najeriya da ke yaki da mayakan Boko Haram a jihohin dake arewa maso gabashin kasar, sun bayyana cewa, sun kara gano tarin makamai daban-daban da mayakan na Boko Haram suka gudu suka bari a wasu gidaje da kuma kewayen garin na Baga.

Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Manjo janar Chris Olukolade wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ya ce, sojojin sun gano makamai da babura da ko dai aka lalata ko kuma mayakan suka gudu suka bari.

Ya kuma bayyana cewa, an yanki soja daya da wuka yayin da aka harbi soja daya a lokacin da suke gudanar da bincike da yammacin ranar Asabar don gano mayakan da suka buya.

Olukolade ya kara da cewa,ana gudanar da bincike kan wasu mutane da suka ce su mazauna garin na Baga ne,don tabbatar da cewa, ba sa yi wa kungiyar ta Boko aiki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China