Dakarun Najeriya sun bayyana cewa, sun kama mayakan Boko Haram da suka yi shigar mata a garin Baga da ke arewa maso gabashin kasar yayin binciken da sojojin suka gudanar .
Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai ya kuma ce dakarun sun yi nasarar gano tarin makamai musamman bama-bamai da mayaka na Boko Haram suka boye a garin na Baga.
Ya kara da cewa, dakarun na ci gaba da damke mayakan da suka buya a garin, sannan ana yiwa wadanda aka kama tambayoyi, baya ga wadanda sojojin suka kama a yayin arangamar da suka yi da mayakan.
Bugu da kari mayakan sama na ci gaba da yin luguden wuta kan maboyar 'yan Boko Haram da ke Gwoza, Bama da dajin Sambisa a kokarin da sojojin ke yi na fatattakar su daga sansanoninsu.
A cewarsa, harin da sojojin ke kaiwa ta sama ya yi nasara matuka, lamarin da ya tilasta wa mayakan Boko Haram din neman mafaka daga luguden wutan da aka kai musu a dajin na Sambisa.