in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya
2015-02-23 16:43:06 cri

Kafofin yada labarun kasar Najeriya sun ba da labari cewa, an kai harin kunar bakin wake a wata kasuwar dake birnin Potiskum na jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar Najeriya a jiya Lahadi 22 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 5, yayin da wasu suka samu raunuka.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe Toyin Gbadegesin ya shaidawa manema labaru ta wayar tarho cewa, wata mace ce ta kai wannan hari a kasuwar Jagwal da ke a birnin Potiskum. Amma bai yi karin haske game da adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, amma kafofin yada labaru sun bayyana cewa, a kalla mutane biyar sun mutu, kuma wasu da dama suka ji rauni.

Ya zuwa yanzu, babu wani mutum ko kungiya da ta sanar da daukar alhakin wannan lamarin.

Idan ba a manta ba, a ran 1 ga wannan wata da muke ciki, an kai makamancin wannan harin a wannan birni, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane shida, yayin da mutane da dama suka ji raunuka. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China