in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An gudanar da gasar Sinanci ta shekarar 2015
2015-03-14 20:29:48 cri

An gudanar da gasar Sinanci ta shekarar 2015 mai taken "Gadar Sinanci", a jami'ar Lagos. Gasar da jami'an ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriyar da karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Lagos da kuma shugabannin kwalejin Confucius na Sin da Najeriya a jami'ar Lagos, da wakilan kamfanonoin masu jarin kasar Sin, har ma da daruruwan dalibai masu koyon Sinanci suka halarta.

Gasar wadda ta gudana a jiya Juma'a 13 ga wata dai ta kasance karo na hudu da aka gudanar da ita a Najeriya. An kuma kasa masu shigar ta zuwa rukunoni uku, wato ajin makarantar firamare, da na 'yan makarantar midil, da kuma ta daliban jami'a, inda suka yi takara a fannoni daban-daban, ciki hadda amsa tambayoyi game da ilimin Sinanci, da rera wakokin Sinanci, da raye-rayen Sinawa da dai sauransu, inda rukunoni 'yan takara kimanin 20 suka shiga gasar.

Da yake tsokaci ya yin wannan gasa, jakada mai kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya Mr Yan Xiangdong, ya bayyana matukar gamsuwa game da kwazon da daliban Najeriyar suka nuna yayin gasar, ya kuma yaba musu matuka.

Kaza lika Mr. Yan ya karfafawa matasan gwiwa game da ci gaba da koyon Sinanci, da kara fahimtar al'adun kasar Sin, matakin da zai taimaka wajen bunkasa mu'ammala tsakanin kasashen biyu a fannin ala'du.

A nata jawabi shugabar kwalejin Confucius ta bangaren kasar Sin farfesa Jiang Lirong, ta bayyana cewa yawan dalibai dake koyon Sinanci a Najeriya yana karuwa sosai. Yanzu haka gaba daya akwai cibiyoyin koyar da Sinanci a jihar Lagos har fiye da 30, inda dalibai fiye da dubu biyar ke koyon Sinanci a wadannan cibiyoyi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China