in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu shirin kafa gwamnatin rikon kwarya, inji shugaban Najeriya
2015-02-23 16:49:03 cri

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, babu wani shiri na kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Shugaba Jonathan wanda ya bayyana hakan jiya Lahadi a Abuja,babban birnin kasar lokacin da ya ke jawabi a babban taron kungiyar Bishop-Bishop ta Najeriya(CBCN) ya kuma shaidawa mahalarta taron cewa, gwamnatin rikon kwarya ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa kuma yana da tabbacin Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa daya.

A cewarsa, gwamnatin soja aka sani da kafa gwamnatin rikon kwarya kuma babu wanda zai amince da ita.

Kalaman shugaba na zuwa ne kwanaki kadan bayan da tsohon shugaban kasar ta Najeriya Ulosegun Obasanjo ya yi zargin cewa,gwamnati mai ci na shirin murda zaben da ke tafe ne ko kuma ta kawo rudanin da zai ba ta damar zama a kan mulki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China